Da dumi dumi ‘yan Bindiga sun kaiwa Jirgin kasan kaduna Abuja Hari.

A wani Rahoto dake Zuwa Mana daga Tsohon Sanatan kaduna ta tsakiya na Cewa an Kai hari was Jirgin Kasa Mai jigilar matafiya tsakanin kaduna da Abuja Kamar yadda Sanatan ya Bayyana a shafinsa na facebook Yana Cewa A daren jiya, ‘yan bindiga sun kai hari kan jirgin Kaduna zuwa Abuja, inda suka dasa wani abin fashewa wanda ya lalata layin dogo tare da farfasa gilashin injin jirgin, sannan suka bude wuta, inda suka nufi Direban da Tankin, lamarin ya faru tsakanin tashar Dutse da Rijana. A daidai Lokacin da Jirgin ke kokarin komawa tashar Rigasa ta Kaduna.

Da

sanyin safiyar nan, ina cikin jirgin lokacin da jirgin namu ya ci karo da wani abin fashewa da ya lalace.
Sanata ya Yi Kira da Cewa a Halin yanzu
Ana bukatar a dakatar da dukkan ayyukan jirgin kasa na Kaduna da ke Abuja na yau har sai an magance wannan matsalar.

wannan labarin na Kai Hari ga Jirgin na Kasa shine na farko tun bayan kafuwar Jirgin Kasan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *