Da’alama hare-haren ‘yan bindiga zai karu a Sabuwar Shekarar 2022 mai zuwa ~Cewar Janar Farouq Yahaya.

Babban Hafsan Sojin kasan Nageriya (COAS), Laftanar Janar Farouk Yahaya, ya yi kira ga kwamandoji daban-daban da su shiryawa yiwuwar karuwar hare-haren ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da sauran miyagun laifuka da ke dagula zaman lafiyar al’umma a shekara mai zuwa.

Ya yi wannan kiran ne jiya a Abuja yayin da yake jawabi ga manyan hafsoshin kasar a wajen rufe taron shekara-shekara na COAS na 2021.

“Dole ne mu kai farmaki ga abokan gaba don murkushe su tare da fatattakar su,” in ji babban hafsan sojojin a cikin jawabinsa ga jami’ai da sojoji masu yaki da rashin tsaro a sassa daban-daban na kasar.

An

kuma bukaci kwamandojin da su samar da tsare-tsare na gaggawa don tabbatar da cewa dakarun sun ci gaba da yin aiki a duk wuraren da suke.

Sannan ya kara da cewa kwamandojin dole ne su tsara yadda zasu inganta gudanarwar su saboda tunkarar ayyukan masu tayar da kayar baya a cikin shekara mai zuwa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilcin babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Iraboh ne ya kaddamar da taron a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa, a yayin taron, mahalarta taron sun tattauna muhimman batutuwan da suka shafi gudanar da ayyukan da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada da kuma samar da kwarewa.

A cewar hafsan sojojin, mahalarta taron sun kuma tattauna batutuwan tsaro daban-daban da suka addabi al’ummar kasar, da suka hada da ayyukan ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda, masu neman ballewa (IPOB) da dai sauransu.

Sakamakon haka, ya yi nuni da cewa, abin da rundunar za ta mayar da hankali a kai a shekara mai zuwa shi ne, samar da karin ayyuka domin ingantattun ayyukan tsaro a fadin kasar.

“Za a ba da fifiko kan horon daidaikun mutane da na sassan da za su inganta aikin hadin gwiwa da kwarewa,” in ji Yahaya.

“A dangane da haka, ina kira ga kwamandojin sojojin Najeriya da su tabbatar sun gudanar da horo na gaskiya a cibiyoyinsu daban-daban don tabbatar da cewa jami’anmu da sojojinmu sun samu kwararewa don tunkarar masu aikata laifuka a filin daga.”

“Bugu da ƙari kuma, kwamandojin dole ne su tabbatar da cewa sojojinsu sun kware wajen gudanar da ayyukan dare da atisayen kwantar da tarzoma ta hanyar gudanar da ayyukan dare masu inganci da horar da ‘yan kwanton bauna.”

Jarida Radio

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *