Dakarun Sojin Nigeria sunyi nasarar kashe mayaƙan ISWAP 24 tare da wasu Kwamandojin ƙungiyar 3; Yaya Ibrahim, Baba Chattimari da Adam Abu Ubaida.

Rahotanni sun tabbatarda aƙalla mayaƙan ISWAP 24 tare da wasu Kwamandoji 3 aka kashe sakamakon luguden wuta da dakarun Sojoji suka yi musu a yammacin ranar Laraba.

Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa nasarar ta Dakarun Sojojin Nigeria tayi sanadiyar mutuwar wasu daga cikin jiga-jigan ƙungiyar waɗanda suka haɗa da; Yaya Ibrahim, Baba Chattimari da Adam Abu Ubaida. Hakazalika babban mataimakin Shugaban ƙungiyar ya raunata sakamakon artabun.

Ɗaya daga cikin Jami’an sirri shine ya zayyanawa Jaridar PRNigeria cewa, a yayinda ƴan ta’addan suke yunƙurin tunkarar Sojojin a dajin Ngamdu, loƙacin ne kuma rundunar Sojin suka yi amfani da jirgin yaƙi na NAF tare da rugurguje ƴan ta’addan.

Sai

dai kuma an tabbatarda mutuwar huɗu daga cikin dakarun Sojojin na Nigeria a yayin artabun.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *