Dole sai an cire siyasa a matakan ɗibar sabbin Jami’an tsaro tare da baiwa jajirtattu dama kafin a samu nasarar murƙushe ta’addanci a Nigeria. ~A cewar Gwamna Zulum

Gwamnan Jihar Borno Farfese Babagana Umara Zulum ya koka bisa yadda aka siyasantar da tsarin ɗaukar sabbin dakarun tsaro a Nigeria.

Zulum ya bayyana cewa abin takaici ne ƙwarai yadda Gwabnoni, Ministoci da sauran masu madafun iko a Gwamnati suka siyasantar da tsarin.

A yanzu samun gurbin karatu a makarantun koyon aikin Sojoji ko Ɗan Sanda ya zama sai wane-da-wane.

Gwamnan ya ƙara da gargaɗin cewa idan har baza’a rinƙa duba jajirtattu yayin ɗaukar sabbin Jami’an tsaro ba dole a cigaba da fuskantar ƙalubale musamman a yunƙurin da ake na magance ta’addanci a Nigeria.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

class="wp-block-gallery columns-1 is-cropped">

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *