Gagarumin ‘dan Bindiga ya Zama Hakimi a Jihar Sokoto.

Ɗan bindiga Bello Turji da yaranshi sunyi juyin mulki a wasu kauyukkan Dake karamar hukumar sabon birnin jahar Sokoto.

Yanran Bello Turji da suka hada da Ɗan Bakkwalo, Boka l Tamiske, Hassan Ɗan Kwaro, DOGO da Jammu Baki sun gayyaci mazauna kauyukkan zaman tattaunawa a kauyen Saturu ranar alhamis 04/10/2021.

Yayin zaman ne suka umurci mazauna kauyen Gangara da su zabi daya daga cikin yan bindigar a matsayin hakiminsu Inda suka zabi dan bindiga Ɗan Bakkwalo a matsayin sabon hakinin gangara.

Nantake

sabon hakimin gangara Ɗan Bakkwalo ya gindiya musu sharudda da suka hada da Bude kasuwanni da masallatai da sauransu.

A kauyen Maƙwaruwa Ɗan bidiga Boka Tamisƙe ya nada kanshin a matsayin hakiminsu Inda ya Kira Taron gaggawa da umurtar hakimin garin Mai suna Ɗan Sani da ya gayawa talakkawansa da Kansa cewa yanzu Boka Tamiske ne sabon hakiminsu ba Shiba.

Yanzu haka su ke da wuka da nama a waddannan kauyukkan.

Rahotan daga DailyStar Nigeria

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *