Haryanzu ‘yan bindiga basu zama ‘yan ta’adda ba a wajen Gwamnatin mu ~Cewar Gwamnatin Tarayya.

Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ya kare matakin gwamnatin tarayya na kin bayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

Ya ce bukatar bin ka’ida ce ta jawo tsaikon.

Magashi, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a, a Maiduguri, yayin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida, ya kara da cewa akwai tsarin da ya kamata a bi kafin a bayyana irin wannan mataki.

“Ba mu bayyana su a matsayin ‘yan ta’adda ba saboda akwai hanyar yin hakan. Idan aka bi hanyar, za a sanya su a matsayin ‘yan ta’adda. Muna jiran a kammala aikin,” inji Magashi.

Kamfanin

Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Ministan wanda ke Maiduguri tare da babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor a ziyarar tantance yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabas, ya bayyana jin dadinsa da nasarorin da aka samu kawo yanzu. rubuta.

Da yake mayar da martani, kakakin kungiyar ta PANDEF, Ken Robinson, ya bukaci Ministan da ya shaida wa ‘yan Najeriya irin wadannan hanyoyin da kuma dalilin da ya sa ba a bi su ba kafin gwamnatin ta haramtawa ‘yan asalin kasar Biafra da sauran kungiyoyi..

Sheikh Ahmad gumi shine Malamin dake Shiga daji domin sulhu da ‘yan Bindigar ko a baya bayan nan malamin ya soki Shirin Gwamnatin Tarayya na ayyana ‘yan Bindiga a amatsayin ‘yan ta’adda Lamarin da malamin Yace Hakan na iya jefa Nageriya cikin Matsala Babba inji Sheikh Ahmed Gumi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *