Hedikwatar tsaro DHQ ta gargadi ‘Yan Siyasa akan amfani da Uniform na Soja a wajen yakin neman zabe.

Hedikwatar tsaro (DHQ) a yau Alhamis ta ce sanya kakin soja da wasu mutane marasa izini da ’yan siyasa ke amfani da su wajen yakin neman zabe haramun ne.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Air Commodore Wap Maigida ya fitar, DHQ ta ce tana takaicin yadda wasu ‘yan siyasa suka rungumi dabi’ar sanya rigar sojoji a fastocin yakin neman zabe.

A takaice dai sanarwar ta ci gaba da cewa, wannan lamari ya sabawa doka, kuma cin zarafi ne baiwa fararen hula damar sanya kakin soji a lokacin atisayen soja.

Commodore

Maigida ya jaddada cewa rundunar sojin Najeriya a matsayinta na rundunar da take da kwararrun jami’ai, abin takaici ya kasance ana amfani da ita a siyasance, don haka ba za ta so a jawo ta cikin kowace irin salon siyasa ba.

A kan haka, DHQ ta shawarci ‘yan siyasa da sauran su da su daina amfani da kakin soji da kayyayakinsu wajen al’amuran siyasa da sauran hada-hadarsu daga yanzu.

Kakakin DHQ ya jaddada cewa duk wanda aka samu da laifin aikata haka za a gurfanar da shi gaban kuliya.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *