Kashe Jama’a A Kaduna: Rahama Sadau Ta Bara..

Fitacciyar Jarumar fina finan Hausa ta kannywood Rahama Sadau Ta tofa albarkacin bakinta akan kashe kashen jama’a da ake yi a Kudancin Kaduna.

Jarumar ta roki gwamnatin Tarayya da na Jihohi da su taimaka su kawo karshen al’amari.

Rahama Sadau tace “Na tsaya ina kalubalantar kashe-kashe a Kudancin Kaduna. Ina kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da su tabbatar da yanayi mai kyau ga dukkan yan Najeriya. Don Allah! ”.

Rahama Sadau Ta fadi hakan ne a shafinta na Twitter, Kuma tuni mabiyanta sukatita yin tsokaci akan kalamin nata, mafi akasari suna nuna yabawarsu ne agareta.

class="sharedaddy sd-sharing-enabled">

Share this:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *