Kisan Gillar Sokoto: A wani salo na kanku akeji ƴan Arewa, Buhari ya tafi ƙaddamar da littafi batare da yakai ziyarar gani da ido ba.

Abu ne da baza’a manta dashi ba a cikin wannan gwamnatin ta shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, akan yadda ƴan bindiga suke cin karen su babu babbaka a Arewacin Najeriya, musamman ma, Katsina, Sokoto, Kaduna da kuma Jihar Niger.

Ko a baya bayan nan, an ruwaito yadda ƴan bindigar suka tare wata mota a can jihar Sokoto, suka kulle kofofin motar sannan suka banka mata wuta, inda mutanen ciki kimanin 42 suka kone ƙurmus tamkar kosai.

class="has-text-align-justify">A ƙasashe da dama, shugabanni kanyi murabus ko kuma barin duk abinda suke domin ganin sun daidai ta lamurran da suka rincaɓe, musamman idan ta kasance lamarin ya jiɓanci tsaro ko kuma rayuwar ƴan ƙasa.

To amma a wannan gwadaben, sai aka ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya cigaba da zuwa rantsar da ayyuka da suka haɗa da ƙaddamar da sabbin jiragen jirgin ruwan yaƙi tare da ƙaddamar da littafin da Chief Bisi Akande ya wallafa.

Haƙiƙa, yin hakan ya bawa mutanen Arewa mamaki, duba da yadda sune suka fi jefawa shugaba Muhammadu Buhari ƙuriar su.

Wasu kuma na mamakin, anya Buharin da suka sani ne kuwa?

Wasu kuma na addu’a ne akan Allah ya karkato dahankalin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi abinda ya dace domin damƙa masa amanar dukiya da rayuwa da mutanen Arewa sukayi.

Wasu kuma babu abinda suke, sai cewa, Allah ya kaimu shekarar 2023.

Ko me hakan yake nufi?Bayyana ra’ayi…

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *