ku murkushe ‘yan Boko Haram da ‘yan Bindiga ~shugaban soja ya sake umarni ga Sojojin Nageriya.

Babban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Farouk Yahaya ya umarci rundunar bataliya ta 4 ta musamman da ke Doma da su ci gaba da jajircewa don ganin sun kubutar da kasar daga hannun mayakan Boko Haram, masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi a Arewa da sauran sassan kasar nan.

Yahaya ya ba da wannan umarnin ne a lokacin da yake zantawa da majiyarmu yayin ziyarar aiki da ya kai hedikwatar bataliyar da ke karamar Hukumar Doma ta Jihar Nasarawa don duba wasu wurare a barikin.

Ya

ce kalubalen tsaro da ke fuskantar kasar nan ba za a iya shawo kansu ba idan ba’a bayarda kulawa da jajircewa daga gwamnatin tarayya ba

CAS, duk da haka, ya gargadi sojojin da su kasance koyaushe suna nuna basira, ladabi da hazaka wajen gudanar da ayyukansu na tsaron ƙasar.

Ya kuma ziyarci babban basaraken gargajiya na yankin, Andoma na Doma, Alhaji Aliyu Onawo Ogah, inda ya bukaci cibiyoyin gargajiya da su yi aiki tare da hukumomin tsaro a jihar.

Andoma na Doma, Alhaji Aliyu Onawo Ogah, ya ce ziyarar ta zo a kan lokaci domin hakan zai karawa mutane kwarin gwiwa kan yaki da laifuka da rashin tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *