Kuje ku kare iyakokin jihohin ku, domin kunfini sanin ƴan ta’addan nan — Buhari ga Gwamnoni.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sako a kan akan gaɓa, zuwa ga Gwamnonin Jihohi daban-daban waɗanda ke fama da matsalar hare-hare daga Fulani makiyaya da ƴan fashi.

Jaridar Mikiya ta tattaro bayanin Shugaban ne a yayin gabatar da wani shiri na musamman a gidan talabijin na Arise TV, a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, inda ya ce Gwamnoni su ne manyan hafsoshin tsaro na jihar su don haka ya kamata su kare ƴan ƙasa daga hare-haren makiyaya da ƴan fashi.

Ya kuma ce ya kamata Gwamnoni su nemi mafita ta din dindin game da matsalar, ya ƙara da cewa ba zai iya kasancewa ko’ina a lokaci ɗaya ba.

Shugaban ya yi iƙirarin cewa Gwamnoni sun fi shi sanin masu aikata laifi a yankinsu, ya ƙara da cewa bai kamata su yi ƙorafin ƙalubalen da suke fuskanta ba.

A cewarsa:

“Kun san waɗannan mutanen fiye da ni, kuma an zaɓe ku ta hanyar dimokiradiyya don kare mutanenku. Don haka, kada ku zauna kuna jiran tsammani zan yi komai, ku ɗauki mataki.”

Zaku iya tuna cewa a cikin ƴan makonnin da suka gabata an samu rahotanni a yankuna daban-daban na ƙasar nan na hare-haren ƴan fashi, inda na baya-bayan nan ya faru a Igangan, Jihar Oyo.

Buhari

Harin ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 20.

Har ila yau, wani harin ya sake afkuwa a jihar Neja wasu makwannin da suka gabata, a harin, an yanka mutane 7 ƴan gida ɗaya.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *