Labarai Cikin Hotuna: Yadda Jami’an tsaro suka kuɓutar da mutane 160 daga dajin ƙare-kukan-ka na Sububu dake jihar Zamfara.

A ƙalla mutane 160 ne aka ceto daga hannun yan bindiga daga cikin dajin Sububu dake ƙaramar hukumar shinkafi ta jihar Zamfara, kamar yadda hukumar ƴan sanda ta jihar bayyana wa manema labarai.

Jami’an tsaron dai sun kuɓutar da mutanen ne ciki harda mata da ƙananan yara a ƙoƙƙobare duk sun rame, wacce hakan ke nunawa duniya sunsha wuya.

class="wp-block-image size-full">

Dajin Sububu dai dake a jihar Zamfara yayi ƙaurin suna a yan kwanakin nan wajen ayyukan masu tada ƙayar baya z duk da irin nasarorin da ake iƙirarin ana samu akan miyagun tan bindiga da suka addabi yankin arewa.

Rundunar tsaro ta hadin guiwa a jihar Zamfara ita ce dai tayi wannan gagarumin aikin na haɗin gwiwa.

Mutanan dake yankin da abinda ya shafa na aikin ceton, sun tabbatar da cewa ceton ya ƙunshi mata da matasa da kuma yara, wadanda aka sace su daga ƙauyukansu, aka yi dajin na Sububu da su.

Allah ya kyauta, sannan ya kawo mana sauƙi na dindindin.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *