Majalisar dattijai ta bawa Jami’an tsaro duk goyon bayan da suke bukata domin wulakanta ‘yan ta’adda ~Cewar Sanata Uba Sani.

Sanata Uba Sani yayi Matukar kaduwa da kisan ‘dan majalisa jiha da ‘yan Bindiga sukayi a Hanyar kaduna Zuwa Zaria a Lokacin da yake aikewa da Sakon ta’aziyyarsa Sanata Malam uba sani yace Na yi matukar kaduwa da kisan gillar da ‘yan ta’adda suka yi wa matashi kuma ‘dan majalisar dokokin jihar Kaduna, Rilwanu Gadagau, a babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya Dole ne a kamo wadanda suka aikata wannan danyen aikin, sannan a nuna musu cikakken nauyin ikon doka.

Santan

ya Kara da Cewa wannan Kashe-kashen baya-bayan nan da ake yi wa ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba a Jihar Kaduna, ba zamu Bar wannan ba a’a dole ne faruwar Hakan a yankin Arewa maso Yamma yasa mu rubanya kokarinmu wajen yakar wadannan ‘yan ta’adda muna fuskantar barazanar wanzuwa tashin Hankali dole mu tashi domin tunkarar wannan ƙalubale Wanda Hakan shine mafi alheri gare mu Baki daya.

Gwamnatin Tarayya, ta hanyar hukumomin tsaro, dole ne ta tsara sabbin dabaru tare da shelanta yaki na Bai ‘daya a kan wadannan abubuwa marasa kyau na son zuciya da rashin son ci gaba. Jin dadin jama’a da tsaron al’umma shi ne babban nauyin da ya rataya a wuyan gwamnati. Dole ne Gwamnatin Tarayya ta tashi tsaye wajen ganin ta tabbatar da tsaron al’ummarmu. Majalisar ta bai wa jami’an tsaro dukkan goyon bayan da ake bukata domin su samu damar wulakanta wadannan miyagun mutane. Abin da muke bukata shine yanke hukunci, ba uzuri ba. Inji shi.

A Karshe Sanatan ya rufe da addu’a Yana Mai Cewa Ina mika ta’aziyyata ga iyalan Hon. Rilwanu Gadagau, gwamnati da al’ummar jihar Kaduna, kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna da ‘yan majalisar dokokin jihar kan wannan rashi da ba za a iya misalta shi ba. Allah ya gafartawa Hon. Gadagau ya bashi aljannar firdausi.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *