Makamai da alburusai guda dubu 178,459 ne suka bace daga ma’ajiyar kayan yaki na ‘yan sanda a shekarar 2019 – Roahoto.

Kimanin nau’ikan makamai da alburusai daban-daban guda 178,459 ne suka bace daga ma’ajiyar kayan yaki na ‘yan sanda ba tare da an tantance su ba a shekarar 2019, kuma ba a bayar da wani rahoto kan inda suke ba, kamar yadda wani rahoton bincike na babban mai binciken kudi na kasa ya bayyana.

A cikin wannan adadi, bayanan sun nuna cewa, akwai bindigogi kirar AK-47 guda dubu 88,078, da bindigu iri-iri guda 3,907 da kuma wasu bindigu daga sassa daban-daban a fadin ƙasarnan da ba za a iya lissafa su ba har zuwa watan Janairun na shekarar 2020.

Cikakken

bayanin makaman da suka bace yana kunshe ne a shafi na 383 zuwa 391 na rahoton shekara-shekara na “Aditor General for the Federation” na rahoton shekara-shekara kan rashin bin ka’ida/ raunin da ya shafi ma’aikatu da da hukumomin gwamnatin tarayyar Najeriya na shekarar da ta kare a ranar 31 ga Disamba, 2019. ” ofishin babban mai binciken kudi ya mikawa majalisar dokokin ƙasarnan.

An gabatar da rahoton ne ga magatakarda na Majalisar Dokoki ta kasa.

Hakazalika, an sanya ranar 15 ga Satumba 2021 kuma babban mai binciken kudi na tarayya, Adolphus Agughu ya sanya wa hannu.

Rahoton ya kuma zargi hedikwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya da rashin cikakkun bayanai kan makaman da ba za a iya amfani da su ba, saboda fargabar cewa irin wadannan na iya fadawa hannun wasu da aka ba su izinin amfani da su ba bisa ka’ida ba.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *