Masu garkuwa da mutane sun bukaci a biya N15m, N20m, N100m ga ma’aikatan karamar hukumar Zariya guda 14sukayi garkuwa dasu.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne masu garkuwa da ma’aikatan kananan hukumomin Zariya su 14 a jihar Kaduna, suka tuntubi wasu iyalai don neman kudin fansa, daga N15m, N20m zuwa N100m ga kowane mutum.

Kakakin Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG), Abdul-Azeez Suleiman, ya tabbatar da hakan jiya a Abuja. Ya ce: “Mun samu labarin cewa wadanda suka yi garkuwa da su sun yi hulda da iyalansu daban a ranar Juma’a.

“Mun samu labarin wadanda suka yi garkuwa da su sun tabbatar wa iyalan wadanda aka kama suna tsaron lafiyar wadanda aka kama kuma sun nemi kudin fansa. A halin da ake ciki, hedkwatar CNG ta kuduri aniyar umurtar reshen daliban jihar Kaduna da su dakatar da zanga-zangar da suka shirya yi, domin kada ta kawo cikas ga sabon ci gaba.

“Muna

tabbatar wa iyalan da abin ya shafa, musamman daliban da suka ji haushi, wadanda ke ba da hadin kai da ‘yan uwansu, wadanda iyayensu na cikin wadanda abin ya shafa, cewa CNG za ta ci gaba da taka-tsan-tsan, game da alkiblar da lamarin zai juya, har sai an dawo da iyayensu da rai.

“Duk da haka, mun fusata kan shiru da hukumomi suka yi a cikin kwanaki hudu da suka gabata, tun lokacin da aka sace wadanda aka kama, wadanda halaltattun ma’aikatan gwamnati ne yayin da suke gudanar da wani aiki,” in ji shi. Kungiyar ta yi kira da a yi addu’a ta musamman domin mayar da duk wadanda aka kama a halin yanzu da ake garkuwa da su a ko’ina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *