MAULUD: Ƴan Nigeria suna fama da yunwa, talauci ga rashin tsaro; ya zama wajibi Gwamnati ta shawo kan waɗannan matsalolin. ~Inji Sheikh Dahiru Bauchi

Shugaban ɗarikar Tijjaniyya kuma babban Malami a Nigeria Sheikh Dahiru Bauchi yayi kira ga Shugaba Buhari da sauran Gwamnonin Jihohin Nigeria akan suyi duk mai yiwuwa wajen ganin an shawo kan matsaloli a Nigeria.

Kamar yadda rahoto ya fito daga Jaridar Daily Post, Shehin Malamin yayi wannan kira ne ayau Talata yayin da ake tsaka da gudanar da shagalin Mauludi a Jihar Bauchi.

Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana cewa, “Shugaban ƙasa da duk Gwamnoni dole suyi mai yiwuwa wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro da garkuwa da mutane.

A cewarsa, babu cigaban da za’a fuskanta muddin babu cikakken tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Har’ilayau;

duk da dubunnan mutanen da suka halarci taron Mauludin, Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana cewa rashin tsaro ya tilastwa mutanen Jihohi daban-daban halartar shagalin na wannan shekarar.

A ƙarshe, Shehin Malamin ya rufe da bayanin yadda talakawa suke fama da yunwa, talauci da kuma rashin tsaro. Don haka yake kira akan Gwamnati tayi duk mai yiwuwa wajen ganin an shawo kan waɗannan matsalolin.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *