Muna tsare da ‘yan ta’adda sama da guda 2,600 wadanda suka mika wuya, amma ba dukansu bane masu laifi, za mu yanke musu hukuncin da ya dace da dokar kasa, in ji gwamna Zullum.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya ce sama da ‘yan tawaye 2,600 da suka mika wuya suna tsare amma ya ce ba dukkan su ne masu laifi ba.

Ya kuma lura cewa sama da mutane 100,000 ‘yan ta’adda suka kashe a Arewa maso Gabas kadai kan rikicin da aka kwashe shekaru 12 ana yi.

Zulum ya fadi hakan ne yayin da yake yiwa manema labarai na fadar gwamnati jawabi bayan ganawa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadar shugaban kasa, Abuja, ranar Talata.

Ya

bayyana cewa da yawa daga cikin wadanda suka mika wuya mata ne da kananan yara wadanda aka tilasta musu shiga cikin masu tayar da kayar bayan. Ya lura cewa da yawa daga cikin su an koya musu amfani da bindigogin AK-47 inda ya kara da cewa za a yanke musu hukuncin da ya dace da dokar kasa.

Gwamnan, duk da haka, ya ce wadanda suka mika wuya za a horar da su don sake hadewa, yana mai cewa, “Babu wata doka da ta ba da shawarar kashe masu tayar da kayar baya wadanda da son ransu suka mika kansu.”

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati za ta yi duk abin da za ta iya don kula da wadanda abin ya shafa, ya kara da cewa, “Ba za a bar su a baya ba.”

Zulum ya ce, “Na zo ne don yi wa Shugaban kasa bayani kan yadda masu tayar da kayar baya ke ci gaba da mika wuya. Ina tsammanin, a wurina, da mafi yawan mutanen jihar Borno, wannan ci gaba ne mai kyau.

“A cikin shekaru 12 da suka gabata, dubunnan rayuka sun salwanta, mutane sun rasa abin rayuwarsu gaba ɗaya. Muna da adadin marayu da zawarawa sama da 50,000; wadannan alkaluma ne na hukuma.

“Adadin wadanda ba na hukuma ba sun fi wannan, kuma mun tasa samun damar noma fiye da kashi uku cikin dari na filayen noman mu saboda tashin hankali, a yanzu ba a san inda kasa da kashi 10 na mutanen jihar Borno suke ba.

“Wannan lamari ne mai matukar mahimmanci kuma ina tsammanin rahoton mika wuya da maharan suka yi, a gare ni musamman da kuma ga mafi yawan mutanen jihar Borno, wani abin farin ciki ne. Sai dai idan muna son ci gaba da yaƙi mara iyaka, ban ga dalilin da zai sa mu ƙi waɗanda ke son mika wuya ba. ”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *