Na kashe mutum biyu: ~Cewar wani Yaro mai shekaru 14 da aka kama cikin ‘yan bindiga a Katsina

Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta yi holen wani yaro mai shekara 14 kuma dan bindiga.

Kakakin yan sandan jihar Katsina Gambo Isah ya ce yaron ya fada musu cewa ya kashe mutane biyu a Mallamawa.

Yaron da aka sakayya sunansa ya ce ya yi nadamar abubuwan da ya aikata kuma yana fatan ya sauya halayensa.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *