Na yi bakin ciki kan kashe Birgediya Janar Zirkusu da wasu sojojin da ‘yan ta’addan ISWAP sukayi – Cewar Shugaba Buhari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da rasuwar Birgediya Janar Dzarma Zirkusu da wasu sojoji uku da aka kashe a wata arangama da ‘yan kungiyar Da’esh ta yammacin Afirka (ISWAP) a jihar Borno.

An kai musu harin ne a nisan kilomita kadan daga garin Askira da ke karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin inda sojoji da ISWAP ke musayar wuta.

Shugaban

kasar a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, ya yaba wa sojojin da suka mutu bisa jajircewarsu, yana mai bayyana sadaukarwar da suka yi a matsayin nuna kauna ga al’ummar kasar.

Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin kasar da iyalan jami’an sojin da suka rasu.

Sanarwar ta ce: “Na yi matukar bakin ciki da jin labarin rasuwar Birgediya Janar Dzarma Zirkusu da sojoji uku da suka bayar da sadaukarwa, a wani abin da ba a saba gani ba, yayin da suke kokarin taimakawa ‘yan uwansu a yakin da suke da ‘yan ta’adda.

“Najeriya ta yi rashin jaruman sojoji. Ina gaishe da jajircewarsu. Allah Ya Jikan su da Rahma. Janar Zirkusu ya bar mu cikin bakin ciki da bacin rai na rashinsa.”

Buhari ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya baiwa Sojojin da iyalan wadanda suka rasu karfin gwiwa da jajircewa wajen jure wannan rashi mara misaltuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *