Rashin tsaro a Najeriya: Buhari na iya bakin kokarin sa – Cewar Osinbajo.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin iya bakin kokarin sa wajen gyara matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Mataimakin ya yi magana ne a yau Alhamis a fadar shugaban kasa a lokacin da ya karbi bakuncin Muhammadu Buhari Osinbajo (MBO) Dynamic Support Group.

Osinbajo ya bada tabbacin cewa za a magance kalubalen tsaro domin samun karfi da girma.

“Shugaban kasa ya kasance mai tsayin daka tare da mai da hankali wajen magance matsalolin kasar nan tun daga kan tsaro.

“Hannu

ne mai tsayayye, ba mai firgita ba, mai mai da hankali, yana kallon al’amuran tsaro a kowace rana, da ƙoƙarin ciyar da mafi kyawun mafita,” in ji shi.

Osinbajo ya jaddada mahimmancin sanin cewa idan ana fuskantar matsaloli, gwamnati na bukatar tallafi daga kowa.

Shugaban ya kara da cewa hadin kan Najeriya na da muhimmanci ga dukkan kabilu da addinai.

“Domin kasar da ke da karfin tattalin arziki a Afirka, ta fara tunanin wargaza kanta.

“Idan kuka rabu, matsalolin za su yawaita, talauci zai karu”, in ji shi.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *