Rundinar Sojojin Najeriya ta Ƙera Saƙaƙo da Zai Dinga Shinshino Bama-Bamai.

Duk da irin ƙalubalen da ake fuskanta na harkar tsaro a ƙasar nan, zaratan sojojin Najeriya basuyin ƙasa a guiwa wajen ganin sun inganta harkar ta tsaro, hakan ne yasa a wannan karon suka samu nasarar ƙirƙirar wani mutum- mutumi mai baiwar shanshana gamida jiyo ƙamshin Bama-Bamai da aka ɓoye a cikin ƙasa ko kuma kaya.

Sojojin Najeriya na gwada saƙakon

class="has-text-align-justify">Rundinar ta sojin Najeriya ta samu nasarar ƙera mutum-mutumin (Robot) ne , biyo bayan dogon bincike da nazari, inda ayanzu dai shi wannan saƙaƙo zai dinga gano bam da aka bunne a cikin ƙasa sannan kuma yayi amfani da dabaru na hikima da aka cusa masa wajen ganin ya wargaza bam ɗin.

Kamar yadda majiyar Mikiya ta tabbatar, yanzu haka za’a miƙa da saƙakon zuwa Arewa maso gabashin Najeriya domin ci gaba da yaƙar gamida daƙile ta’annatin da ƴan ta’addan Boko Haram suke cigaba da ƙaddamar wa a yankin.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *