Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Abdulsalami Abubakar, da Sarkin Musulmi zasu gana akan waɗansu abubuwa masu muhimmanci gobe.

Idan dai za’a iya tunawa, yanayin tsaro a ƴan kwanakin nan ya ta’azzara matuƙa, abinda yasa masu hannu dumu dumu a sha’anin tsaro suke ta fama domin ganin an samu maslaha mafi dacewa a ƙasar, wato zaman lafiya.

Hakan shine yasa, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Abdulsalami, da Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar II suka yanke hukuncin zama akan teburi domin bankaɗo dalilai da kuma maganin abin daya addabi ƙasar.

Taron dai kamar yadda takardar gayyata ta bayyana tun a yau 9, ya nuna ana sa rai cewar za’a gudanar dashi ne a ranar Alhamis 10 ga wata, acan Transcorp Hilton dake Abuja.

Masu halartar sun haɗa da Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya wato Abdulsalami Abubakar, da tsohon shugaban cocin katolika wato John Onaiyekan.

A cewar wasu majiyoyin Mikiya na ɓoye, batutuwan da suka shafi haɗin kan ƙasa, tsaro, zaman lafiya, farfado da tattalin arziki, da ci gaba na daga cikin abubuwan da za a tattauna a taron gobe

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *