Sojoji ne suka kawo Karin hare-haren ta’addanci a jihar Sokoto ~Cewar Tambuwal.

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya zargi sojoji da kai hare-haren ‘yan bindiga da aka kora daga Zamfara zuwa jiharsa.

An samu karuwar hare-haren ‘yan bindiga a Sakkwato a ‘yan kwanakin nan amma harin da aka kai a makon jiya ya ba wa mutane da dama mamaki, musamman yadda ‘yan Bindigar Suka kona fasinjoji. wanda ya faru a kan hanyar Sabon Birni zuwa Isa a cikin garin Sokoto, majiyarmu ta shaida mana yadda wasu gungun ‘yan bindiga da ake kyautata zaton na goyon bayan wani sarkin ‘yan ta’adda ne mai suna Bello Turji suka bude wuta kan motar bas din da suke ciki har sai da ta Kama da wuta.

Matar

data tsira ‘yar shekara 30 ta ce ta kalli ‘ya’yanta hudu da mahaifiyarta da wasu ‘yan uwanta uku suna kone kurmus.

Jim kadan bayan tattaunawar, matar ta rasu ne a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Danfordiyo da ke Sakkwato, inda take jinya sakamakon raunukan da ta samu a harin.
Tambuwal dai ya je yankin da harin ya faru ne amma bayan ya fita sai ‘yan bindiga suka mamaye al’ummar tare da bindige mutane uku.

A lokacin da gwamnan ya karbi tawagar manyan jiga-jigan Gwamnati da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike zuwa jihar sakamakon tashe tashen hankulan, Tambuwal ya alakanta karuwar hare-haren da Operation Hadarin Daji, da sojoji suka yi a Zamfara.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *