Sojojin Nigeria sun kashe mayaƙan Boko Haram da ISWAP 37 a dajin Sambisa.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Rahotanni sun tabbatarda cewa dakarun Sojin Nigeria sun kashe aƙalla mayaƙan Boko Haram da ISWAP 37 a wani ruwan wuta da suka yi a sansanin ƴan ta’addan.

Wannan yana ƙunshe cikin wani jawabi da mai magana da yawun rundunar Sojin Nigeria, Onyema Nwachukwu ya bayyana ga manema labaru jiya Lahadi.

Mista Nwachukwu ya bayyana cewa da dama daga cikin ƴan ta’addan sun raunata bayan waɗanda aka kashe.

Sashin rundunar Sojin da akayiwa laƙabi da Ofareshon “HAƊIN KAI” sun ɗauki loƙaci suna shawagi domin gano mafakar ƴan ta’addan yayinda a ƙarshe bayan dogon loƙaci akayi amfani da jiragen yaƙi wajen tarwatsa mafakar ƴan ta’addan dake a dajin Sambisa.

An

kuma bayyana cewa kusan mayaƙan 50 aka hango suna tattaunawa a wata maɓoya, yayinda Sojojin Nigeria sukayi dirar mikiya a kansu, daga nan ne kuma aka kashe aƙalla ƴan ta’addan mutum 37.

A ƙarshe, Mista Nwachukwu ya rufe da cewa Sojojin Nigeria za su cigaba da ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen ta’addancin Boko Haram da ya ɗauki loƙaci yana faruwa a Jihar Borno da sauran Jihohin Arewa maso gabashin Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *