Ta’addanci, garkuwa da mutane, tada kayar baya, da kuma rikicin addini da na kabilanci sune manyan kalubalen da ke addabar dimokradiyyar kasarnan – Magashi.

Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya), a ranar Juma’a ya bayyana cewa karuwar kalubalen tsaro a fadin kasarnan ne ya sa ake tura sojoji cikin aikin tsaro cikin gida.

Magashi, ya yaba da kokarin da sojojin musamman ma rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ke yi na mayar da hankali kan ci gaban aiki domin magance matsalolin tsaro da ke addabar kasarnan.

Ministan ya bayyana hakan ne a wajen bikin yaye hafsoshi 13 na Kwalejin Yakin Sojan Sama na ranar 7/2021 da aka gudanar a Nigerian Airforce Offices mess, Makurdi.

Ministan

wanda ya samu wakilcin daraktan harkokin soji na ma’aikatar tsaro ta tarayya, Sunday Musa, ya ce ta’addanci, garkuwa da mutane, tada kayar baya, da kuma rikicin addini na kabilanci sune manyan kalubalen da ke addabar dimokradiyyar kasarnan.

Ya ce tare da yanayin yakin da ke haifar da sabbin kalubale ga jami’an tsaro ya zama dole a kirkiro sabbin dabaru da hanyoyin zamani don tunkarar kalubalen.

Ya ce, “A halin yanzu kasarmu tana fama da kalubale daban-daban na tsaro, wadanda suka hada da ta’addanci, tada kayar baya, ‘yan fashi da makami da kuma garkuwa da mutane. Hakazalika, ana kuma gwada dimokaradiyyar mu ta rigingimun kabilanci da kuma rikicin manoma da makiyaya.

“Wadannan ƙalubalen sun haifar da sakamako mara kyau ga albarkatun ɗan adam, saboda haka, aka shiga tsakani da shigar da sojoji cikin aikin tsaro na cikin gida a duk faɗin ƙasarnan.”

Tun da farko, babban hafsan hafsoshin sojin sama Air Marshal Oladayo Amao, ya bayyana cewa kwalejin yaki da sojojin sama wadda ita ce jami’ar horar da sojoji mafi girma a NAF tana taka rawar gani wajen samar da horo mai ma’ana da kuma bunkasa karfin dan’adam wanda daya ne daga cikin jiga-jigan jami’o’in samar da ayyukan yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *