TSARIN NIN: Sheikh Pantami ya gaza gano ‘yan ta’adda tare da dakatar da ta’addanci a Arewacin Nageriya.

Kusan shekara guda kenan da da Gwamnatin Tarayyar ta bayarda sanarwa tare da umarnin toshe dukkan wasu layukan Sadarwar da ba’a yi rijistarsu da lambobin katin zama ‘dan Kasa NIN ba.

Sai dai Bincike da shedun gani da Ido na Cewa haryanzu bamu wata Cikakkiyar nasara da tsarin NIN number ‘din ya kawo duba da yadda sha’anin ta’addanci ke cigaba da gudana a Nageriya musamman arewacin Nageriya dake fama da ‘yan ta’addan Boko Haram da ‘yan Bindiga masu garkuwa da Mutane da barayin shanu, a Lokacin da ministan Sadarwar Farfesa Ali Isa Pantami ya gabatar da wannan sanarwa Jama’ar Nageriya na cike da murna bisa tunanin Cewa ministan ya kamo hanyar kawo karshen ta’addancin da ake fama dashi a wannan Kasa ta Nageriya.

A

Lokacin ministan yace haramun ne ka bude account na banki Babu NIN.

Haramun ne layukan waya Babu rijistar NIN.

Haramun ne katin zabe babu NIN.

Haramun ne ka biya rebano da biyan fansho ba tare NIN ba.

Haramun ne Kuma laifi kana tsarin aikin Gwamnatin Tarayya baka da NIN numa Babban Laifi ne da ka’iya kaika Gidan yari a cewar Minisatan sadarwa Ali Isa Pantami a Lokacin sanarwar.

Bayan wannan sanarwa Jama’ar Nageriya sun shiga baraza tare da Shiga yanayin hanzari Zuwa ga cibiyoyin da za’ayi musu rijistar NIN nasu domin gujewa taka Dokar Gwamnati.

Gwamnatin Tarayya ta bullo da wannan shirin ne domin kawo karshen ta’addancin Dake faruwa a Nageriya saii dai kawo yanzu tsawon kusan Shekara guda kenan da aiwatar da shiri Amma Babu abinda ya canja game da sha’anin farmakin ta’addancin ‘Yan Bindiga.

Bayan kaddamar da NIN an sace Dalibai sittin da uku 63 a yawuri dake jihar Kebbi.

‘Yan Bindiga sun sace Dalibai mutun dari Shida 600 a kankara dake jihar katsina.

An sace Dalibai talatin da Tara 39 a jihar kaduna

An sace Dalibai mutun dari uku 300 a Makarantar Jangebe Dake Jihar zamfara.

Da Sauran wuraren da ban da ban wa’yanda aka sace wasu Kuma aka kashe su ba tare da an kubutar da rayuwar su ba wanda Kuma haryanzu tsarin rijistar NIN number Bai Tabbatar mana a bayyana Cewa an kamo Yan ta’addan masu garkuwa da Mutanen dake wannan aika-aika ba.

Idan baku manta ba dai A ranar 15 ga Disamba, 2020, Gwamnatin Tarayya ta ba da sanarwar cewa bayan 30 ga Disamba, 2020, za a toshe duk layukan da ba su yi rijista da ingantattun lambobin NIN ba akan hanyoyin su na kamfanonin sadarwa ba.

Daga baya ta tsawaita daga ranar 30 ga Disamba, 2020 zuwa 19 ga Janairu, 2021.

Ya ba da karin makonni shida ga masu yin rajista ba tare da NIN ba daga 30 ga Disamba, 2020 zuwa 9 ga Fabrairu, 2021 sannan ya kara tsawaita makonni takwas a ranar 2 ga Fabrairu, 2021 amma kungiyoyi da yawa sun yi kira da a kara tsawaita wa’adin ko dakatar da tsarin rajista na NIN.

Bincike ya nuna Cewa haryanzu dai akwai layukan da Basu anfani da tsarin rijistar na NIN Kuma ba a kulle masu layukan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *