TSARO: Sufeto-Janar na ƴan Sanda, Usman Alkali ya naɗa sabbin Kwamishinoni 13 zuwa waɗansu Jihohi a Nigeria.

Sufeto-Janar na ƴan sanda, IGP Usman Alkali ya naɗa sabbin Kwamishinoni a Jihohi 13 tare da babban birnin tarayya Abuja.

Hakan ya fito ne cikin wani saƙo na musamman da mai magana da yawun rundunar yan Sanda ta ƙasa, Frank Mba ya bayyana.

Ya ƙara da cewa waɗannan sabbin naɗe-naɗe suna da alaƙa da yunƙurin hukumar ƴan Sanda na ganin an samar da isasshen zaman lafiya tare da magance ayyukan ɓata gari a lungu da saƙon Nigeria.

Jihohin da suka rahauta da waɗannan sabbin Kwamishinoni sun haɗa da:

1- Jihar Niger, CP Monday Bala Kuryas.
2- Jihar Kwara, CP Emienbo Tuesday Assayamo.
3-

Jihar Nassarawa, CP Soyemi Musbau Adesina.
4- Jihar Taraba, CP Abimbola Shokoya.
5- Jihar Benue, CP Akingbola Olatunji.
6- Jihar Kogi, CP Arungwa Nwazue Udo.
7- Jihar Kaduna, CP Abdullahi Mudashiru
8- Jihar Jigawa, CP Aliyu Sale Tafida.
9- Jihar Enugu, CP Abubakar Lawal.
10- Jihar Cross River, CP Alhassan Aminu.
11- Jihar Bayelsa, CP Echeng Eworo Echeng.
12- Jihar Bebbi, CP Musa Baba
13- FCT Abuja, CP Babaji Sunday.

Sauran Jami’an ƴan Sandan da aka naɗa sun haɗa da; CO Ndatsu Aliyu tsohon Kwamishinan ƴan Sanda a Jihar Enugu, wanda yanzu aka naɗa a matsayin Jami’in kula da ayyukan damfara FCID reshen Abuja. Sai kuma CP Sikiru Akande a matsayin Jami’i mai kula da fannin ICT wacce take da helkwata a Abuja. Sai CO Bankole Lanre a matsayin Kwamishin INTERPOL reshen Jihar Lagos. Sai kuma CP Augustine Arop wanda aka naɗa a matsayin mataimakin Kwamanda a babbar Kwalejin ƴan Sanda dake a birnin Jos ta Jihar Filato.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *