Tun mun shaida juna, ku gaggauta dawo da makamai da alburusai da kuka sata — Kwamishinan ƴan sanda ga ƴan ta’adda.

CP Abutu Yaro

Kwamishinan ƴan sanda mai kula da jihar Imo, CP. Abutu Yaro ya faɗawa ƴan daba da kuma ƴan fashi a jihar da su dawo da dukkan bindigogin ƴan sanda da suka sace waɗanda suke hannunsu.

Kwamishinan ya ce rundunar ta yanke shawarar maganin duk wani mutumin da aka kama da irin waɗannan makamai da alburusai.

Yaro, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba a wata tattaunawa ta musamman da wakilinmu, ya ce bindigogin ƴan sanda da yawa sun yi batan dawo sakamakon awon gaba da su da aka yi a yayin zanga-zangar EndSARS da hare-hare da aka ƙaddamar wa da ƴan sanda a ƴan kwanakin nan.

Bugu da ƙari, ya danganta harbe-harben da kashe-kashen da aka yi a jihar a kwanan nan ga ƴan fashin, inda yace hakan ya biyo baya ne sakamakon sace bindigogi da makamai na ƴan sanda da sukayi sakamakon zanga-zangar.

Ya kuma yi kira ga iyaye da masu ruwa da tsaki kan son zaman lafiya da su kai rahoton duk wani yaro da ke hannunsu da duk wata bindiga ta ƴan sanda da suka gani.

A cewar sa:

“Ina kira ga iyaye da masu kyakkyawar manufa ta jihar da su kai rahoton duk wani yaro a yankinsu da yake da bindigar ƴan sanda. Bindigar ƴan sanda ta ƴan sanda ce ba ta wani mutum ba.”

CP Abutu Yaro

“Da yawa daga cikin ofisoshin ƴan sanda in za’a iya tunawa an kona su kwanan nan kuma bindigogin da suka tafi da su, da su ne ake amfani wajen harbe-harbe da kashe-kashen da akeyi a jihar kwanan nan, “in ji Yaro.

Kwamishinan, amma ya ce ƴan sanda a jihar ba za su bar kowani mai laifi ya tafi salin alin ba, kuma hukumar ƴan sanda bazatayi ƙasa a gwuiwa ba don ganin cewa an magance matsalar fashi da kuma hukunta su lokacin da aka kama su.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *