Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun cinna wa Gidan Yarin Ikoyi da ke Jihar Legas wuta tare da sakin fursunoni.

Mai magana da yawun gwamnan Jihar Legas ya tabbatar da labarin. Tuni ‘yan sanda da sojoji suka isa wurin domin dakile harin.

A yau da misalin ƙkarfe 12:00 na rana ne tsagerun suka fara kai hari kuma shaidun gani da ido sun ce sun ji ƙkarar harbe-harbe.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta batun tserewar fursunoni ta bakin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta najeriya.

Shi ma Gidan Yarin Okitipupa da ke Jihar Ondo, an kai masa hari inda aka saki fursunoni a yau Alhamis din nan.

Rahotanni

sun bayyana cewa fursunoni kusan 60 ne suka tsere yayin harin, kuma aka ƙkona ababen hawa.

Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan wasu masu zanga-zanga sun ɓalle gidajen yari biyu a Jihar Edo tare da sakin fursunoni masu yawa.

Wannan Zanga zangar ta #EndSars ce ta Jefa Kasar Cikin Mummunan yanayi Na Fuskantar Barazanar Tsaro.

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *