Wasu ‘yan bindiga sun kai hari matsugunin Fulani a jihar Neja, sun kashe mazauna garin tare da kona gidaje.

Akalla mutane tara ne suka mutu yayin da aka kona gidaje lokacin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari a matsugunin Fulani a karamar hukumar Mashegu ta jihar Neja.

Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa harin ya afku ne a ranar Litinin din da ta gabata inda wasu ‘yan bindiga da dama dauke da makamai suka mamaye yankin inda suka bude wuta kan Fulani makiyaya.

Rahotanni

sun ce barayin sun tafi shanu da ba a tantance adadinsu ba, da wasu kayayyaki masu daraja da suka hada da babura.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar PPRO, Kwamishinan ‘yan sanda a jihar ya tura tawagar kwararru zuwa yankin domin dakile ci gaba da kai hare-hare tare da lalubo wadanda suka kai harin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya yi kira ga mazauna jihar da su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da suka dace domin rundunar tana kokarin maido da zaman lafiya a duk wuraren da ake fama da tashe-tashen hankula.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *