Wasu ‘yan bindiga sun kai hari matsugunin Fulani, sun kashe daya, sun tafi da shanu a Kaduna.

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani mutum mai suna Imam Abubakar, a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a wani kauyan Fulani a unguwar Barakallahu da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

‘Yan bindigar da ba a san ko su waye ba a lokacin harin, sun tafi da wasu shanu da ba a bayyana adadinsu ba.

Hakimin unguwar Alhaji Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:15 na safe a safiyar yau.

Ya

bayyana cewa, “da tsakar dare ne muka fara jin karar harbe-harbe, tabbas (’yan bindiga) sunyi harbi har sau 50 kafin daga bisani su bar unguwar.”

Hakimin ya ci gaba da bayanin cewa an shaida masa cewa (’yan bindiga) sun kashe mutum daya tare da kwashe shanu da dama.

Ya ce har yanzu bai tabbatar da adadin ba yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa ganin iyalan.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, ya ce za tuntubi DPO mai kula da yankin.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *