WATA SABUWA: Ina ji a raina cewa lalacewar al’amura a Nigeria yana da alaƙa da kisan kiyashin da aka yima wasu mutane 2015 a Zaria ~Cewar Sheikh Maqari

Farfesa Maqari ya bayyana cewa yana ji a ransa cewa taɓarɓarewar al’amura musamman ta ɓangaren tsaro a Nigeria yana da alaƙa da kisan kiyashin da akayiwa wasu mutane a Zaria.

Maqari ya bayyana hakane cikin wani faifan bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta mai tsawon mintuna biyar da aka wallafa, kuma yayi wannan jawabi ne a jiya Asabar yayinda yake gabatar da tafsiri a babban masallacin centre dake Abuja.

Shehin Malamin ya kuma nuna takaicinsa bisa yadda mutanen a wancan loƙacin su ka yita murna bayan da aka kashe mabiya mazhabar Shi’a.

Tare

da cewa, “koda kuwa waɗanda aka kashe masu bautar wuta ne, bai kamata al’umma suyi ta murna ba duba da yadda Allah Ya haramta zubar da jinin ɗan Adam.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *