YAƘI DA TA’ADDANCI: Dakarun Sojojin Nigeria sun samu nasarar kashe ɗaya daga cikin Jagororin ISWAP mai suna Abou Sufyan.

Gwabzawar dakarun Sojin Nigeria da ƴan ta’adda tayi silar mutuwar ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar ISWAP mai suna Abou Sufyan.

Jaridar PRNigeria ta wallafa cewa jiragen yaƙin NAF ƙarƙashin ofareshon Haɗin Ƙai sune suka rugurguza sansanin na ƙungiyar ISWAP dake ƙauyen Kusuma a ƙaramar hukumar Marte ta Jihar Borno.

Da yawa daga cikin mayaƙan sun tsere kafin daga bisani a samu nasarar hallaka ɗaya daga cikin Jagororin na ISWAP.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *