‘Yan Bindiga sun kashe Mutane sittin da biyu 62 a kasuwar Goronyo dake Jihar Sokoto.

Rahotanni daga Jihar Sokoto na cewa ‘Yan ta’adda, wadanda galibi ake kiransu’ yan fashi, sun mamaye kasuwar Goronyo da ke jihar Sokoto, inda suka kashe mutane sama da 60.
An ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun kutsa cikin kasuwar da misalin karfe 5 na yamma a ranar Lahadi, inda suka rika harbin kan mai uwa da wabi.

A cewar Daily Star, wata jarida mai tushe a Sakkwato, ta bayar da rahoton cewa ‘yan bindigar sun yi ta’addanci na kusan sa’o’i biyu ba tare da fuskantar turjiya daga jami’an tsaro ba, wanda ba a iya sanar da su harin ba sakamakon rufe Kamfanonin sadarwa a yankin.
A

cewar majiyoyi daga Karamar Hukumar, an kirga gawarwaki kusan arba’in kamar daren Lahadi.

Sabbin bayanai daga wasu mazauna Goronyo sun tabbatar wa DailyStar cewa tuni aka ajiye gawarwaki 62 a Babban Asibitin Goronyo da safiyar Litinin, wannan baya ga wasu gawarwakin da ‘yan uwansu suka tafi da su don yin jana’iza.

Majiyoyin sun kuma shaidawa jaridar cewa har yanzu ba a ga wasu da yawa ba yayin da suke ƙoƙarin tserewa ta hanyar shiga cikin daji a yayin Harbe harben

Bamu samu damar magana da ‘yan Sanda ba a kawo Yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *