‘Yan Boko Haram sun kai mummunan hari Damasak, sun kwashi kayan tallafin’yan gudun hijira, sun bankawa sauran wuta da wasu wuraren a Borno.

Boko haram sun kai mummunan hari Damasak sun kwashi kayan tallafin ‘yan gudun hijira sun bankawa sauran wuta da wasu wuraren a Borno.

‘Ya kungiyar nan ta boko haram sun kai hari garin Damasak a Jihar Borno, sun kwashi kayan tallafi kuma sun bankawa ragowar wuta, sun kuma kone gurare da dama.

Daraktan NRC Na Najeriya, Eric Batanon ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ya ce 5 daga cikin ma’aikatan su sun tsere dakyar.

Ya kara da cewa maharan sun yi nasarar bankawa ma’ajiyar kayan tallafawa al:umma wuta tare da lalata ababen hawa da illata direbobin su.

Sannan ya yi kira ga gwamnatin tarayya cewa kayan tallafawa jama’a na raguwa a Arewa maso gabas, don haka suna neman gwamnati da ta agaza musu da taimako.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *