‘Yan Boko Haram Sun Zo Wajena, Na Tsira Daga Sharrinsu, Rayuwata Tana Cikin Hadari – Inji Mailafia.

Wani tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Obadiah Mailafia, ya yi ikirarin cewa rayuwarsa na cikin hadari.

“Inda na sauka, a ranar Alhamis, na ga wasu baƙon mutane a ƙofar suna ƙoƙarin kutsawa.

Na yi tsalle daga shingen na tsere saboda ban san ko su wanene ba,” in ji shi.

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gayyaci Mailafia a watan Agusta, kan zargin da ya yi cewa wani Gwamnan Arewa ne shugaban kungiyar Boko Haram.

Jaridar Newspot ta rawaito cewa bayan gayyatar sa ta DSS karo na biyu, sashin binciken manyan laifuka na ‘yan sanda a Abuja, sun nemi ya bayyana a gaban ta.

Amma

Mailafia ya ki girmama gayyatar sai dai ya shigar da kara yana neman umarnin hana a gayyatar sa da ‘yan sanda suka yi.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a Jos, babban birnin jihar Filato, bayan da hukumar DSS ta yi masa tambayoyi a karo na uku, Mailafia ya ce yana ta samun barazana a rayuwarsa.

“Na nuna cewa ina da dalili na yarda cewa rayuwata ta shiga cikin hadari. “Ba ni da wata cikakkiyar hujja amma ina fuskantar barazana, ana ta kirana.

“Inda na sauka, a ranar Alhamis, na ga wasu baƙon mutane a ƙofar suna ƙoƙarin kutsawa.

Na yi tsalle daga shingen na tsere saboda ban san ko su wanene ba,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *