‘Yan Majalissu Basu Isa Su Tsige Hafsoshin Tsaro Ba~Fadar Shugaban Kasa.

A yau fadar shugaban kasa tace majalisar dokoki data dattijai basu isa su tsige hafsoshin tsaron Nigeria ba, shugaba Buhari ne kadai yake da ikon nadawa da saukewa don haka babu Wanda ya isa ya tsige su se shugaba Buhari.

Martanin fadar shugaban kasar ya biyo bayan furucin da yan majalisun tarayyar Nigeria guda biyu suka nemi hafsoshin tsaron Nigeria da su sauka daga kan mukaman su tunda sun Gaza kawo karshen matsalar tsaron da ake fama da ita a cikin kasar.

Yaya kuke kallon wannan musayar yawun tsakanin fadar shugaban kasa da kuma majalisun dokokin Nigeria.?

Daga

Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *