‘Yan Sanda sun kubutar da jami’in soja da mutun sha biyar 15 daga hannun ‘yan Kungiyar ta’addancin Boko Haram.

Tawagar ‘yan sanda da ke sintiri kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, a ranar Litinin din da ta gabata sun hana wasu mahara yin garkuwa da wani soja da matafiya 15.

Sojan, Lance Corporal, yana tare da Bataliya 4, Marte.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Borno, ASP Sani Kamilu, ya ce lamarin ya faru ne a kusa da kauyukan Yanakiri da Kondori, yayin da wasu mahara dauke da manyan motoci kusan 20 suka yi wa masu motocin kwanton bauna.

Wasu

da ake zargin ‘yan ta’adda na Boko Haram ne suka tare su, suka yi awon gaba da su cikin daji.

“Tawagar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar ‘yan sandan Rapid Response Squad kan samun bayanan sun bi sahun wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne suka shiga cikin daji.

Bayan musayar wuta, an kubutar da wadanda harin ya rutsa da su saboda karfin wuta da dabaru da jami’an ‘yan sanda suka yi,” in ji Kamilu.

Sai dai ya ce uku daga cikin matafiya ba a gansu ba harzuwa Yanzu.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *