‘Yan Ta’adda Sun Kashe Mutane Dayawa A Kaduna.

An tattaro cewa rukunin ‘Yan Ta’addan sun kai hari kan alumma tun da sanyin safiyar Alhamis (yau).

Wata kungiyar Fulani da ake kyautata zaton ita ta kai hari a yankin Kurmin Masara a karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna, inda suka kashe mutanen da ba a tantance yawansu ba.

Rukunin ‘yan ta’addan sun kai hari kan alumma tun da sanyin safiyar Alhamis (yau).

Har zuwalokacin hada wannan rahoto ba a gano gawar ko da mutun daya a wurin ba, Saboda Maharan sun sun kone gidaje da dama yayin harin.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ba da sanarwar kafa dokar hana fita ta awanni 24 a karamar hukumar da abin ya shafa a watan Yuni na wannan shekara domin dakile matsalar kazamin fadan, amma duk da wannan yunkuri ana ci gaba da samun kashe-kashen a yankin.

class="sharedaddy sd-sharing-enabled">

Share this:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *