Yanzu na tabbata zaman lafiya ya dawo a ko’ina cikin nageriya ~Cewar ministan tsaro Bashir Magashi.

Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ya sake nanata kudirin gwamnatin tarayya na ci gaba da samar da isassun kayan aiki ga rundunar sojin don gudanar da ayyukan da aka basu.

Magashi ya bayar da wannan tabbacin ne a wajen liyafar Samun ‘yancin kai ga membobin rundunar soji, wanda hedkwatar tsaro ta shirya ranar Asabar a Abuja.

Ya yaba wa sojoji kan kokarin su wanda yace ya zuwa yanzu na tabbatar da cewa zaman lafiya ya dawo a kowane bangare na kasar, in ji Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya.

Ya

kuma ce Shugaban kasa, Muhammadu Buhari (mai ritaya) zai ci gaba da tabbatar da cewa an kula da jin dadin ma’aikatan yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *