YANZU-YANZU: Ƴan Bindiga sun afka Jami’ar Abuja tare da sace wasu daga cikin ma’aikatan makarantar.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Rahotanni sun tabbatarda cewa ƴan bindiga sun sace waɗansu daga cikin ma’aika a Jami’ar Abuja.

Al’amarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Talata.

Shaidar gani da ido, mai suna Dzarma Idris ya bayyana ga Jaridar Daily Trust cewa da misalin ƙarfe 12:15am ƴan Bindigar suka fara harbe-harbe a yankin, daga busani kuma ɗalibai da sauran ma’aikatan kowa ya tsere.

A nasa ɓangaren, mai magana da yawun Shugaban ƴan Sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh ya bayyana cewa a halin yanzu suna cigaba da bincike bisa ga a’lamarin.

Kawo yanzu dai ba’a san adadin ma’aikatan da ƴan Bindigar suka sace a Jami’ar ta Abuja ba.

class="wp-block-gallery columns-1 is-cropped">

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *