YANZU-YANZU: Ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutane 60 a Jihar Zamfara.

Rahotannin da suke shigowa yanzu sun tabbatarda ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutane 60 a ƙauyen Kadawa dake ƙaramar hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.

Kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta wallafa, shaidun gani da ido sun bayyana yarda ƴan Bindigar suka mamaye ƙauyen tun da misalin ƙarfe 6:00pm na yammacin jiya Alhamis harzuwa safiyar yau Juma’a.

Kawo yanzu dai an rasa mutanen da za’a tattaru ayiwa gawarwakin jana’iza, domin duk kan al’ummar ƙauyen sun tsere domin tsira da rayukan su.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *