Za mu kunyata ƴan Bindiga, kuma zamu tabbatar da kare rayukan al’umma. ~Shugaba Buhari ya aikewa da Gwamna Tambuwal saƙo.

Shugaba Muhammadu Buhari yayi alƙawarin Gwamnatinsa cewa zata zaƙulo ƴan bindigar da suke cin zarafin al’ummah tare da cigaba da baiwa al’umma kariya.

Shugaba Buhari ya bayar da wannan tabbaci ne yayinda ya tura wakilai na musamman domin su jajantawa Gwamna Tambuwal bisa ga kisan matafiya 42 da ƴan bindiga suka yi a Jihar Sokoto.

Har’ilayau, wannan yana ƙunshe cikin wani jawabi na musamman da mai magana da yawun Gwamna Tambuwal, Muhammad Bello ya bayyana a yau Asabar.

Tawagar

da Buhari ya tura ta samu wakilcin mai bawa Shugaban ƙasa shawara ta fannin tsaro wato Babagana Monguno.

Shugaba Buhari yayi godiya bisa ga irin tarbar da Gwamna yayi ga wakilan da aka tura zuwa Jiharta Sokoto domin jajantawa.

Buhari cikin saƙon da ya aikewa da Tambuwal ya bayyana cewa kisan rayuka babban abin takaici ne, kuma zaiyi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin an kare rayukan al’ummar Jihar Sokoto da Nigeria baki ɗaya.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *