Bakusan nine na koyawa mawaƙi Micheal Jackson rawa ba, kuke cewa ina wuce makaɗi da rawa wajen rawa ta — Mawaƙi mai ƙaramin jiki irin na tsigi tsila wato “Grand P”

Grand P

Idan ana maganar rawa da lanƙwasa jiki gamida jijjiga salon nishaɗi tare da karkaɗa ko ina, idan akace Micheal Jackson, sai kawai ayi shiru, domin tun sanda yake raye da kuma yanzu bayan mutuwar sa, masana sunyi ittifakin cewa ba’a samu wanda yakai shi iya rawa salon “subargado” ba watau rawa samfurin kiɗan “POP“.

To sai gashi, wani faifan bidiyo na wannan shahararren mawaƙin na ƙasar Guinea wanda aka fi sani da Grand P mai kantamemiyar budurwar wacce take yar asalin ƙasar Ivory Coast wato Eudoxie Yao, ya fito yana wata magana wacce tabawa kowa mamaki.

class="wp-block-image size-full">
Grand P

Shi dai mawaƙin ya kasance yana da jiki dan ƙarami ne, amma ɗauke da manyan abubuwan mamaki. Domin koda budurwarsa ƙatuwar halitta ce, sannan ya taɓa cewa yana so ya tsaya takarar shugaban ƙasar Guinea.

A wannan karen ya ɓara, inda ya ƙara cewa, shine ya koyawa mawaƙi Micheal Jackson rawa, sanda yana raye. Ga kalaman Grand P:

“Yauwa, ku saurare ni dakyau. Na daɗe ina karanta abubuwan da kuke faɗa a kaina a sada zumunta na zamani akan salon takun rawa ta.”Kunce wai idan ina rawa, ina wuce sautin, bama tafiya tare. Ba haka bane sam.

Grand P

“Wai bakusan nine na koyawa Micheal Jackson rawa ba lokacin yana yaro? , Ku tambayi masana rawa!!!.

“Shin ku kuntaɓa rawa ne ma a rayuwar ku? To dan kuji, kowa yana rawa ne daidai da yanda yake ra’ayi. Haka shine tsarin”.

Grand P

Mawaƙin mai zubin tsigi tsila, ya ƙara da cewa:

“A rayuwa , kamata yayi mutanen da suke faɗan haka su maida hankali akan abu mai muhimmanci bawai rawa taba”.

Duk da dai mawaƙin yayi abin ne a wani salo na barkwanci da kuma wasa, to amma da alama yana yin hakan ne saboda yadda ake masa dariya da kuma tsokanar sa kafafen sadarwa na zamani akan yadda salon rawarsa take.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *