Da ‘dumi ‘dumi tsohon Gwamnan babban bankin Nageriya CBN Soludo na Jam’iyar APGA ya lashe Zaben jihar Anambra.

Bayan kafa tarihi da yayi a Najeriya a matsayin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya da ya taba zama gwamnan jiha, Charles Soludo ne ya yi nasara a zaɓen gwamna inda ya cinye ƙananan hukumomi 19 cikin 21 na jihar.

Wannan zaɓe gwajin waye ya fi ƙarfi ne tsakanin jam’iyyun APGA, APC da PDP a jihar Anambra.

Sanin kowa ne cewa APGA ce jam’iyyar da tunda aka kafa ta take yin nasara a zaɓen gwamnan jihar Anambra. Ana yi mata da laƙabi da jam’iyyar Ojukwu wand shine ya kafa ta.

Bayan

sanar da ‘Inkonkulusib’ da hukunar zaɓe ta yi ranar Lahadi, ranar Talata aka gudanar da zaɓen a karamar hukumar Ihiala da ba ayi zaɓe ba ranar Lahadi.

Ɗan Takarar APGA, Soludo yayi nasara a zaɓen inda ya sami kuri’u sama da 8000, APC 343 sai kuma PDP da ta samu kuri’u dubu biyu da ɗori.

Da take sanar da sakamakon zaben Malamar Zabe, Florence Obi, ta bayyana Charles Soludo da yin nasara a ƙananan hukumomi 19 cikin 21.

Soludo ya samu kuri’u 112,229 a zaɓen, shi kuma Valentin Ozigbo na PDP ya samu kuri’u 53,807 wanda shine ya zo na biyu a zaɓen amma kuma tsakanin sa da Soludo akai ratar kuri’u sama da 58,000.

Duk da gwamnati da APC ke taƙama da shi a tsakiya, bai yiwa dan takaran ta Andy Uba tasiri ba. Daidai da ƙaramar hukuma ɗaya bai iya samun koda rabin kuri’un da aka kaɗa a karamar hukuma ɗaya ba.

YPP duk da ba asan ta sosai ba amma ta iya cinye karamar hukuma ɗaya, itama jam’iyyar PDP ta samu karamar hukuma ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *