Da duminsa: Shugaba Buhari zai kaddamar e-Naira ranar Litnin, eNaira wani sabo kudin Najeriya ne

Shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da tsarin gwajin kudin intanet da aka yiwa lakabi da eNaira Abubuwan da ya kamata ku sani tsakanin kudin intanet na Najeriya fadar Aso Villa, ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2021.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana hakan a jawabin da Diraktan labarai na bankin, Osita Nwanisobi, ya saki ranar Asabar.

A ranar 1 ga Oktoba, CBN ya shirya kaddamar da eNaira amma aka dakatar saboda wasu matsaloli.

Jawabin

yace: “Biyo bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki wanda ya hada da bakunan Najeriya, masana tasarrufin kudin zamani, yan kasuwa da wasu yan Najeriya, za’a fara amfani da kudin da CBN ta tsara daga ranar Litinin, 25 ga Oktoba, 2021.”

“CBN shirya take da tabbatar da cewa kowa ya samu eNaira kamar yadda ake samun kudin takarda.”

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *