Gwamnonin arewa ne suka kawo talauci Jahilci da rashin tsaro ~Cewar Ibrahim Umar Musa.

Babban aikin kowacce irin gwamnati shine kare rai, lafiya da dukiyar al’umma, wanda wadannan suna daga cikin kudure kudure na majalisar dinkin duniya domin ganin zaman lafiya ya samu acikin kowacce irin al’umma a fadin duniya, tareda magance matsalar talauci, jahilci da kuma bawa kowa dama acikin al’umma.
Kowa yasan halin da Nigeria take ciki na talauci, jahilci da rashin tsaro a bisa wasu dalilai, wanda daya daga cikin dalilan shine rashin bawa kananan hukumomi damarsu, kamar yadda dokar kasa ta tanada.


Gwamnonin

Nigeria sunyi watsi da wancan kundi na dokar Nigeria wajen danne hakkin kananan hukumomin tareda tasarrafi da kudadensu, babban takaici shine kananan hukumomin a wasu jahohin na Nigeria basa iya yin kananan ayyuka wanda ya shafi rayuwar al’umma kai tsaye, misali gyaran kananan asibitoci tareda zuba magunguna, gyaran makarantu primary da basu tallafi na kayan karatu da rubutu, taimakawa hukumomin tsaro nasa kai (‘yan kwamati) da kayan aiki da alawus domin kare lafiya da dukiyar al’umma. gyaran kwalbati, rijiyar burtsatse, da shimfida hanyoyi acikin unguwannin talakawa da sauran ayyuka masu amfani ga al’umma.


Haka nan bangaren gina dan adam ta hanyar koyawa al’umma sana’a tareda basu jari, samawa al’umma ayyukanyi tareda basu tallafi akan abinda ya shafi harkar ilimi, lafiya da harkokin yau da kullum.
Idan har gwamnonin Nigeria zasu sakarwa kananan hukumomi mara kamar yadda doka ta tanada, ina kyautata zaton zasu taimaka wajen rage matsalar talauci daya addabi Nigeria, saboda kowacce karamar hukuma a Nigeria zata iya samawa mutum 300 aikinyi kowanne wata ta hanyar koya musu sana’a da bada jari.


Rashin aikinyi da talauci shine silar daya haifar da jahilci da rashin tsaro acikin Nigeria.
Gwamnonin Nigeria sunsami kudade da damarmaki a wajen gwamnatin tarayya mai yawan gaske wanda ya kamata ace sun taimakawa shugaban kasa Muhammad Buhari domin cimma burinsa na magance matsalar tsaro, samarda aikinyi ga matasa, amma abin yaci tura, saboda yadda suka maida kananan hukumomi kamar asusunsu na jaha.
Ina kira ga gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Muhammad Buhari akan su dauki mataki mai tsaurin gaske wajen bawa kananan hukumomin Nigeria iskar ‘yanci, saboda da hadin kan kananan hukumomin ne kadai za’a cimma buri da muradin wannan gwamnatin.

Allah Ya bamu lafiya da zaman lafiya da kwanciyar hankali da karuwar arziki a Nigeria bakidaya, Ameen Ya Rabbi.

Daga Ibrahim Umar Musa
Kawu Gama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *