Jami’ar tarayya dake Dutse (FUD) ta ƙaryata hotunan da ake yaɗawa cewa wasu ɗalibai suna zagaye Shugaban ɗaliban makarantar SUG yayinda yake zuwa ɗakin karatu.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Hukumar gudanarwar Jami’ar tarayya dake Dutse, FUD ta ƙaryata hotunan da suke zagaya shafukan sada zumunta cewa ana raka Shugaban daliban makarantar wato SUG zuwa ɗakin lakca da Jami’an tsaro.

Jami’in yaɗa labarai na musamman dake a Jami’ar ta Dutse mai suna Abdullahi Yahaya Bello shine ya sanar da hakan ayau Alhamis.

Ya bayyana cewa waɗanda aka gani da baƙaƙen kaya zagaye da Shugaban ɗaliban mai suna Muhammad Mukhtar Umar, ɗaliban sashin koyon ilimin fannin tsaro ne wato “Criminology” kuma sunyi hakan ne domin gwajin yadda suke koyo a fannin amma ba domin bashi kariya ba.

Bazai

taɓa yiwuwa hukumar makaranta ta bar wasu ɗalibai kawai domin su rinƙa baiwa Shugaban ɗalibai fadanci ba.

A ƙarshe, Abdullahi ya rufe da cewa taken Jami’ar ta Dutse shine koyon madarar ilimi da kakykyawar ɗabi’a, don haka bazai yiwu hakan ta faru a sashin makarantar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *