Jami’ar Tarayya Lokoja Ta Dauko Mafarauta 60 Domin Samar Da Tsaro A Harabar Jami’ar.

Mataimakin shugaban jami’ar tarayya ta Lokoja (FUL), Farfesa Olayemi Akinwumi, ya dauki nauyin mafarauta 60 domin karfafa tsaro a jami’ar.

Akinwumi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai don bikin fara taron tarukan cibiyar karo na biyar wanda aka shirya yi a ranar Litinin 8 ga watan Nuwamba zuwa Lahadi, 14 ga Nuwamba, 2021.

Ya kuma kara da cewa mafarautan su 60 za su kara kaimi ga kokarin ‘yan sanda da jami’an tsaron farin kaya (NSCDC) wajen samar da isasshen tsaro na rayuka da dukiyoyi ga dalibai da ma’aikatan jari’ar da harabar makarantar.

Ya

kuma tabbatar wa da iyaye cewa cibiyar ba za ta bar kowa a baya ba wajen samar da ingantaccen tsaro don tabbatar da rayuwar dalibai da ma’aikata a babban harabar jami’ar.

Ya kara da cewa ba za a kwashe daliban zuwa dakunan kwanan dalibai ba har sai jami’an hukumar sun gamsu da tsarin tsaro na cibiyar, yana mai cewa yanayin dakin karatun ya bukaci a damu.

“Masu gudanar da wannan cibiya ba za su yi wasa da tsaron dalibai da ma’aikatan jami’ar ba. Mun ga abin da ya faru kwanan nan a wasu manyan makarantun kasar nan inda aka yi garkuwa da Farfesa da ‘ya’yansu a harabar jami’o’in.

“Mun dauki mafarauta sama da 60 kuma sun tsare wuraren da masu aikata laifuka za su yi amfani da su a matsayin hanyar tserewa kuma za mu toshe wuraren. Har sai mun gamsu da tsaro a nan wurin dindindin na jami’ar, ba za mu kwashe dalibai zuwa dakunan kwanan dalibai ba,” inji shi.

Da yake jawabi a wajen taron, mataimakin shugaban jami’ar ya bayyana cewa, za yaye dalibai 804 da suka kammala karatun digiri na biyu da digirin digirgir, inda ya ce za a kuma bayar da digirin girmamawa ga fitattun mutane da suka bayar da gudunmawa sosai ga ci gaban Nijeriya.

Mataimakin shugaban jami’ar wanda ya bayyana cewa karancin kudade ya kasance babban kalubalen da jami’ar ke fuskanta ya bayyana cewa cibiyar ta samu ci gaba sosai da sauri ta fuskar shirye-shiryen ilimi, ci gaban ababen more rayuwa, bincike da kirkire-kirkire.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *