JIHAR KANO: Na kusa fasa kwai nan bada jimawa ba — Muhuyi

Hambarren tsohon Shugaban hukumar yaki da ta’annati gamida yiwa kasa zagon kasa na jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado yace a shirye yake ya daki gefen faranti akan wasu al’amuran gwamnatin jihar Kano da Dr. Abdullahi Umar Ganduje yake jagoranta.
Muhuyi ya sanar da haka ne jiya a wata hira ta musamman da zanta da gidan raiyon Freedom mai zaman kansa dake jihar Kano.

class="has-text-align-justify">Kamar yadda Muhuyin ya zayyana, dalilin da yasa aka dakatar dashi daga shugabancin hukumar daya jagoranta bai wuce dalilin da kin ya amince a tafka wata al’mundahanar wasu kudade ba.

A cewar sa:


Lokacin da aka dakatar dani daga hukumar, kudin da nake dashi, bai wuc naira dubu saba’in da uku ba, kuma a ranar da za’a kore ni, sai dana samo kudaden da aka iya aiwatar da kukumar kafin na bar ofishin”.

Ni bana tsoron duk wani bincimken da ake yi akaina, domin kuwa babu tsoron wani abu da nake, duba da yadda na san ina da tarin shaidu da hujjoji akan zargin da akace aqna yi min’ Inji Muhuyi.

Bugu da kari, Muhuyi ya kara da cewa:

Duk wasu abubuwa da kuka sani ina da kwafi domin su zamar mun shaidaq, in ba don haka ba, ban isa na zio nayi wannan hirar ba, kuma tuhuma ta da ake yi taba mutunci na ne, domin kuwa babu wanda bai san ina zuwa ganin likita ba’.

Idan za’a iya tunawa, a baya bayan nan nan ne dai gwamnatin Kano ta sauke Muhuyi daga mukaminsa, wanda a yanzu ake gudanar da bincike bisa zargew-zargen da ake yi masa a lokacin da yake shugabantar hukumar.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *